Home Labaru Kisan Kawo: ‘Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Yi Wa Abokan Sa...

Kisan Kawo: ‘Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Yi Wa Abokan Sa Ihun Masu Garkuwa Da Mutane A Kaduna

936
0

Rundunar ‘yan sandan jihar kaduna ta kama Musa Imam wanda ya yi ihun karya a kan masu garkuwa da mutane za su sace shi a unguwar Kawo da ke Kaduna, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku.

Abokanan Imam sun biyo shi ne tun daga jihar Lagos, bayan sun tsaya mishi a matsayin shaidu a kotu ya samu beli, sai ya gudo Kaduna, bayan zuwan su gadar Kawo sai ya yi ihun cewa mutanen suna so su sace shi ne.

Ihun na shi ke da wuya, sai hankalin mutanen da ke wurin ta tashi, inda nan ta ke suka kona motar da mutanan su ke ciki, wanda haka ya sa mutane biyu da ke cikin motar suka shiga gidan mai da ke kusa da inda lamarin ya faru, sai ‘yan sanda suka kwace su da kyar.

A kokarin jami’an tsaro na ganin sun fita da mutanen daga gidan mai, sai hakan ya yi sanadiyyar harbin wasu mutane uku.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar kaduna DSP Yakubu Sabo ya fitar, ya ce sun samu nasarar kama Alhaji Musa Imam a yammacin ranar Talatar da ta gabata.

Sanarwar ta kara da cewa, mutum daya da jami’an tsaron suka harba a lokacin da su ke kokarin ceto ran sauran mutane biyu ya mutu, wanda hakan ya sa adadin mamatan suka zama uku.

Yakubu sabo ya ce, ‘yan sandan jihar Legas sun kira mutanen uku da suka tsayawa Alhaji Musa Imam a matsayin shaidu kuma suka biyo Kaduna domin tafiya da shi, shi kuma ya na ganin su sai ya fara yi musu ihun barayin mutane wanda hakan ya haifar da wannan mummunan al’amari.

Leave a Reply