Home Labaru Wazirin Katsina Ya Yi Murabus Daga Kan Kujerar Sa

Wazirin Katsina Ya Yi Murabus Daga Kan Kujerar Sa

92
0

Wazirin Katsina Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya yi murabus daga majalisar masarautar Katsina, biyo bayan tuhumar da majalisar ta yi ma shi cewa ya tattauna batutuwan rashin tsaro a birnin Ilorin na jihar Kwara ba tare da yardar masarautar ba.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne Farfesa Lugga ya halarci wani taro a Ilorin, inda ya ce yawan hare-haren ‘yan bindiga sun yi sanadiyar rufe makarantu a kananan hukumomi takwas na jihar Katsina.

Farfesa Lugga, ya ce lamarin ya kai ga har hakiman kananan hukumomin takwas sun koma cikin birnin Katsina da zama sakamakon hare-haren, sai dai hakan bai yi wa majalisar masarautar Katsina dadi ba, inda ta aike ma shi da tuhuma.

Yayin da ya ke martani a kan tuhumar, Farfesan ya amsa lamurra uku da majalisar ke tuhumar sa a kai, sannan daga bisani ya gabatar wa Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardar ajiye sarautar sa.