Home Labaru Kotu Ta Umarci A Ba Mohammed Adoke Dama Ya Tafi Neman Lafiya...

Kotu Ta Umarci A Ba Mohammed Adoke Dama Ya Tafi Neman Lafiya Amurka

53
0

Babar Kotun tarayya da ke Abuja, ta amince da rokon tsohon Atoni Janar Mohammed Adoke na neman izinin tafiya kasar amurka domin duba lafiyar sa.

Yayin da ya ke yanke hukunci, Alkalin Kotun mai shari’a Inyang Ekwo, ya ba da umarnin a bada Fasfon Mohammed Adoke domin ya samu damar neman Biza.

Mai shari’a Ekwo, ya kuma umarci Muhammed Adoke ya maida Fasfon cikin kwana uku da zarar ya dawo gida Nijeriya.

An da gurafanar da Adoke gaban Kotu ne bisa tuhume-tuhumen da su ka shafi almundahana da kuɗaɗen gwamnati.

Tuni dai an gabatar da Fasfon Mohammed Adoke gaban Alkali, a wani ɓangare na cika sharuɗɗan Belin da Kotun da ba shi tun farko.