Home Labaru ‘Yan Nijeriya Da Ke Kasar Ukraniya Sun Ce Gwanda Su Mutu Da...

‘Yan Nijeriya Da Ke Kasar Ukraniya Sun Ce Gwanda Su Mutu Da Su Dawo Nijeriya

159
0

Wasu ‘yan Nijeriya mazauna kasar Ukraniya, sun yi watsi da ikirarin gwamnatin tarayya na kwaso su daga kasar sakamakon yakin ta da Rasha, inda wasu ‘yan Nijeriya ke cewa sun gwammace yaki ya ci su da su dawo gida Nijeriya.

Wani dan Nijeriya da ya dade a birnin Kiev, Edidiong Ukpakha, ya ce duk maganar da gwamnatin Nijeriya ke yi ba gaskiya ba ce, domin ba ta cika alkawurra, kuma babu abin da za ta yi saboda jirage a yanzu ba su tashi a kasar.

Ya ce ya na zaune a kasar Ukraine tun a shekara ta 2013, lokacin wani rikici irin wannan, kuma an yi alkawarin kwashe ‘yan Nijeriya amma ba a yi ahakan ba.

Wani dalibi mai suna Treasure Chinenye Bellgam, ya ce abin da gwamnatin Nijeriya ke kokarin yi ya na da matukar kyau, amma

mafi akasarin ‘yan Nijeriya kudi su ka je nema, kuma ba za su yarda su dawo Nijeriya ba, hasali ma sun gwammace su mutu a can maimakon su dawo gida.