Home Coronavirus Wata Sabuwa: Buhari Ya Sake Tsawaita Wa’adin Kwamitin Yaƙi Da Cutar Korona

Wata Sabuwa: Buhari Ya Sake Tsawaita Wa’adin Kwamitin Yaƙi Da Cutar Korona

157
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake tsawaita wa’adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da annobar korona zuwa ƙarshen watan Maris na shekara ta 2021.

A wani saƙo da shugaba Buhari ya wallafa a shafin sa na Twitter, ya ce ba zai yiwu ci-gaban da aka samu na watanni tara da su ka gabata ya tafi haka nan ba.

Ya ce ya tsaya ya yi nazari a kan lamarin, kuma ya aminci cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaugawa wajen daƙile yaɗuwar cutar korona. Shugaba Buhari, ya kuma yi kira ga masu sarautun gargajiya da malamai su ba kwamitin haɗin kai wajen wayar da kan al’umma game da cutar.