Home Labaru Kuma Dai: Jami’an Tsaron Nijeriya Sun Gaza Kare Matafiya — Zulum

Kuma Dai: Jami’an Tsaron Nijeriya Sun Gaza Kare Matafiya — Zulum

194
0

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya ce akwai sauran aiki a gaban jami’an tsaro na kare lafiya da dukiyoyin al’umma

Zulum ya bayyana haka ne, yayin da ya ke tsokaci a kan halin da matafiya ke ciki a jihar Borno da sauran jihohin Nijeriya.

Ya ce babban abin takaici ne a ce Jami’an sojin Nijeriya sun gaza kare matafiya, yadda munmunar aika-aikar ke faruwa a kan hanyar zuwa garuruwan Sakana da Auno, wadanda ke da tazarar kilomita 20 kacal. Gwamna Zulum ya kara da cewa, akwai jami’an tsaro da aka girke a kan hanyar, amma ba su gudanar da aikin su yadda ya kamata, sai dai su kafa shinge domin karbar kudi daga hannun matafiya.