Home Labaru Ta’addanci: Za Mu Ga Bayan Masu Garkuwa Da Mutane Don Neman Kudin...

Ta’addanci: Za Mu Ga Bayan Masu Garkuwa Da Mutane Don Neman Kudin Fansa — Burutai

110
0
Ba Za Mu Fasa Shirin Binciken Matafiya Su Nuna Katin Shaida Ba - Buratai

Shugaban rundunar sojojin Nijeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, ya umurci sojojin da ke fage daga cewa kada su daga kafa har sai sun ga bayan ‘yan ta’addan da ke addabar jama’a.

Don ganin an kawo karshen wannan matsala, Burutai ya kara wa’adin aikin dakarun da ke aiki domin kawo karshen ‘yan ta’addan zuwa watanni uku na farkon sabuwar shekara.

Janar Buratai, ya ce karin wa’adin dai ya zo ne, a daidai lokacin da hare-haren ‘yan ta’adda ke kara hauhawa, don haka ya ce ya na ganin idan aka kara shi za su iya samun nasarar murkushe su nan ba da jimawa ba.

Wani masani a fannin tsaro Dr. Kabir Adamu,  ya ce ya na ganin ba tun yau ya kamata a dauki kwararan matakai mamaye dazuzzuka ba, kuma ana iya cimma nasara idan an yi amfani da na’urorin zamani, musamman wajen amfani da jirage masu saukar angulu.

Ya ce idan aka yi la’akari da kasashen da su ka cigaba a duniya, su kan yi amfani da waddanan na’urorin wajen magance matsalolin da su ke cikin dokar daji.