Home Labaru Wata Sabuwa: Buhari Ya Sake Nada Emiefile A Matsayin Gwamnan CBN

Wata Sabuwa: Buhari Ya Sake Nada Emiefile A Matsayin Gwamnan CBN

219
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya nada Godwin Emiefile a matsayin gwamnan babban Bankin Nijeriya karo na biyu.

Hakan kuwa ya biyo bayan kammala wa’adin sa na farko ne da zai cika ranar 2 ga watan Yuni na shekara ta 2019.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya karanta wasikar neman hakan, wadda shugaba Buhari ya aika ma su.

Idan Majalisar ta tabbatar da nadin Godwin Emiefile dai, zai cigaba da zama gwamnan Babban bankin Nijeriya har tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Leave a Reply