Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nemi kotu ta yi watsi karar da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP su ka shigar, bisa zargin cewa hukumar zabe tare da hadin bakin jam’iyyar APC da hukumomin tsaro sun murde zaben da su ka lashe sun ba shugaba Buhari.
Lauyan shugaba Buhari Wole Olanipekun, ya ce shugaba Buhari ya aika da takardar bukatar ta shi ne a ranar 16 ga watan Afrilu.
A cikin takardar, shugaba Buhari ya bukaci kotu ta yi watsi da saurarrn karar Atiku, saboda ba shi da takardun da ya kamata a ce ya zama shugaban Nijeriya kamar yadda dokar kasa ta tsara.
Alkalin kotun daukaka Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa, ta ce maganganun jama’a ne za su yanke hukunci a kan karar da ta ke saurare.
You must log in to post a comment.