Home Labaru Garambawul: Gwamnatin Filato Za Ta Ruguje Wani Sashe Na Babbar Kasuwar Jos

Garambawul: Gwamnatin Filato Za Ta Ruguje Wani Sashe Na Babbar Kasuwar Jos

286
0

Gwamnatin Jihar Filato ta bada sanarwar cewa a ranar 19 Ga Mayu za ta rushe, tare da kone wani sashe na Kasuwar birnin Jos, kamar yadda Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Yakubu Datti ya bayyana.

Sanarwar, ta kuma shawarci wadanda duk ke zaune a tsawon mita 200 daga kasuwar su gaggauta ficewa nan da ranar 17 Ga watan Mayu.

Rahotanni sun ce za a hana zirga-zirgar ababen hawa a dukkan hanyoyin da su ka doshi kasuwar, kuma za a rufe su saboda tabbatar da tsaron rakuya da dukiyoyin jama’a.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnati na bada hakuri a kan duk wata takuwarawa da jama’a za su fuskanta sakamakon wannan aiki da za a yi.

Yakubu Datti ya kara da cewa, gwamnati na ci-gaba da daukar dukkan wasu matakai da su ka wajaba, don ganin an sake gina kasuwar a cikin yanayin da jama’a ba su tagayyara ba.

Leave a Reply