Home Labaru Wata Sabuwa: An Dage Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna

Wata Sabuwa: An Dage Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna

43
0
Gwamnatin Kaduna ta ba jami'an tsaro umurnin daukar mataki kan masu karya dokar hana fita saboda coronavirus
Jihar Kaduna ta nuna bacin rai bisa yadda jama'a ke karya dokar hana fita.

Shugabar hukumar zabe ta jihar Kaduna SIECOM Dr. Saratu Dikko Audu, ta bayyana dage zaben kananan hukumomin jihar zuwa ranar 4 ga watan Satumba na shekara ta 2021.

Dr. Saratu Dikko Audu, ta bayyana haka ne a helkwatar hukumar, yayin wani taro da su ka gudanar a Kaduna.

Tun farko dai an shirya gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansilolin ne a ranar 5 ga watan Yuni na shekara ta 2021, kafin daga bisani a dage zuwa ranar 14 ga watan Augusta na shekara ta 2021.