Home Labaru Ambaliya: Ganduje Ya Gwangwaje Iyalan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Da Tallafin...

Ambaliya: Ganduje Ya Gwangwaje Iyalan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Da Tallafin Kudi

29
0

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bada tallafin Naira dubu 200 ga kowanne daga cikin iyalan mutane 18 da ambaliyar ruwa ta kashe a Doguwa.

Ganduje dai ya kai ziyarar musamman ne domin ta’aziyya ga iyalan mamatan, inda ya yi addu’ar samun rahama ga waɗanda su ka rasu sanadiyyar ruwan sama mai tsanani.

Ya ce a lokacin da su ka samu labarin sun kaɗu sosai, don haka su na addu’ar Allah ya gafarta ma waɗanda ruwan ya tafi da rayuwar su.