Home Labaru Matsalar Tsaro: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Rediyo Nijeriya A...

Matsalar Tsaro: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Rediyo Nijeriya A Oyo

51
0

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a gidan Rediyo Nijeriya da ke Moniya a birnin Ibadan na jihar Oyo, inda su ka lalata motoci da gilasan jikin kofa da na tagogin da ke ginin ma’aikatar.

Rahotanni sun ce, maharan sun kai harin ne domin ɗaukar fansa, biyo bayan wani farmaki da jami’an tsaro su ka kai maɓoyar a yankin Sasa ranar Asabar da ta gabata.

Yayin harin da jami’an tsaron sa-kai na bijilanti da mafarauta su ka kai wa ‘yan bindiga, sun kashe masu mutum ɗaya, lamarin da yay a sa su ka yi fushi tare da kai hari gidan rediyon, inda su ke tsammanin mafarautan na da ofishi.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Oyo Adewale Osifeso ya tabbatar da kai harin a cikin wata sanarwa da ya fitar.