Home Labaru Wasu Tsaffin Gwamnonin Arewa Sun Bada Gudunmawa Wajen Samun Karfin Yan Ta’Adda

Wasu Tsaffin Gwamnonin Arewa Sun Bada Gudunmawa Wajen Samun Karfin Yan Ta’Adda

90
0

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, ya zargi wasu
tsofaffin gwamnonin yankin Arewa maso Yamma da cin
amanar ƙawancen da jihohi su ka ƙulla domin samar da tsaro.

Rahotannji sun ambato Gwamnan ya na cewa, tsofaffin gwamnonin sun yi wa ƙawancen zagon ƙasa ne ta hanyar hulda da ‘yan bindiga.

Ya ce ɗaukar irin waɗannan hanyoyin marasa kyau ne su ka janyo arewa ta wayi gari cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da mummunar tabarbarewar tsaro.

Gwamma Uba Sani ya ƙara da cewa, kirkirar ‘yan sandan jihohi ne hanya ɗaya tilo da za ta iya kawo karshen kalubalen tsaro a Nijeriya.

Leave a Reply