Home Labaru Gwamnonin APC Sun Goyi Bayan Takarar Abbas

Gwamnonin APC Sun Goyi Bayan Takarar Abbas

153
0

Shugaban Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC Hope
Uzodinma, ya ce kungiyar ta na goyon bayan Tajudeen Abbas
a takarar Shugaban Majalisar Wakilai.

A wata sanarwa da kwamitin yakin zaben Abbas ya fitar, Uzodinma ya ce gwamnonin sun kuduri aniyar mara wa Benjamin Kalu daga jihar Abia baya a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai.

Mista Uzodinma ya bayyana haka ne, lokacin da ya karbi bakuncin tawagar yakin neman zaben Abbas da Kalu, inda ya ce jam’iyyar ta yi zabi mai kyau na mutanen da za su jagoranci majalisar wakilai.

Gwamna Uzodinma, ya yaba wa ’yan kungiyar da su ka fito daga jam’iyyu takwas, sannan ya taya su murnar nasarar da su ka samu a zaben da ya gabata.

Tun farko Tajuddeen Abbas ya yaba wa kungiyar bisa goyon bayan da su ka ba shi, ya na mai jaddada aniyar shi ta ganin an kafa majalisa ta 10.

Leave a Reply