Home Labaru APC Na Zargin Kwankwaso Da Sayar Da Kadarorin Jihar Kano

APC Na Zargin Kwankwaso Da Sayar Da Kadarorin Jihar Kano

69
0

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, ta ce tsohon Gwamnan
jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya saida wasu filayen
gwamnati da sauran kadarori lokacin da ya ke riƙe da jihar
tsakanin shekara ta 1999 da 2003 da kuma 2011 zuwa 2015.

APC ta ce baya ga filayen gwamnati da aka saida a wasu sassan Kano, gwamnatin Kwankwaso ta kuma saida wasu kadarorin gwamnatin jihar da ke Abuja da Legas.

Jam’iyyar APC ta yi zargin haka ne a wani taron manema labarai da ta shirya a sakatariyar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Kano.

Da ya ke jawabi a wajen taron, Mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na jihar Shehu Maigari, ya ce babu
mutuntawa game da rushe gine-ginen da gwamnatin Kano ke ci-gaba da yi a jihar, ya na mai cewa matakin ya taba harkokin miliyoyin ‘yan asalin jihar.

Leave a Reply