Home Labaru Wakilci: An Biya ‘Yan Majalisun Dokoki Na Tarayya Biliyoyin Kudaden Alawi

Wakilci: An Biya ‘Yan Majalisun Dokoki Na Tarayya Biliyoyin Kudaden Alawi

212
0

‘Yan majalisun dokoki na tarayya sun samu kudin maraba da zuwa majalisa da ya kunshi alawus-alawus na gida da na kayan daki.

Wata kwakkwarar majiya ta ce, ‘yan majalisar sun fara samun kudaden ne tun daga ranar 5 ga watan Yuli na shekara ta 2019.

Majalisar dattawa

Majiyar ta cigaba da cewa, yayin da Sanatoci su ka karbi naira miliyan 30 kowannen su, ‘yan majalisar wakilai kuma sun tashi da naira miliyan 25.

Jimillar kudaden da sanatoci 109 su ka karba dai ya kama naira biliyan 3 da miliyan 300, yayin da na ‘yan majalisar wakilai 360 kuma ya kai naira biliyan 9.

Wani dan majalisar wakilai da ya bukaci a sakaya sunan shi, ya ce a ciki akwai kudin kama gida a Abuja kimanin Naira miliyan 4, da kudin kayan daki Naira miliyan 3 da dubu 900, sai kuma kudin motar hawa Naira miliyan 7 kuma an ba kowa.

Sai dai wani rahoton jaridar Herald ya bayyana cewa, akasarin sabbin sanatoci sun nuna bacin ran su a kan wadannan kudade cewa sun yi kadan.