Home Home Tun Kafin Rana Ta Take Tsaka Atiku Zai Lashe Zaɓe – Rundunar...

Tun Kafin Rana Ta Take Tsaka Atiku Zai Lashe Zaɓe – Rundunar Kamfen Ɗin Atiku

453
0
Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar da Okowa, ta bugi gaban cewa jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar ne za su lashe zaɓen shekara ta 2023 tun da sanyin safiya.

Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar da Okowa, ta bugi gaban cewa jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar ne za su lashe zaɓen shekara ta 2023 tun da sanyin safiya.

Kakakin Yaɗa Labarai na kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Kola Ologbondiyan ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a Abuja.

Ologbondiyan, ya ce irin yadda Atiku Abubakar ke samun ɗimbin masoya, alama ce mai nuni da cewa tun kafin a yi nisa da fara jefa ƙuri’a Atiku zai lashe zaɓen shekara ta 2023.

Ya ce Atiku ya samu goyon bayan kusan mafi yawan ‘yan Nijeriya, waɗanda ma ba su cikin rukunin da masu yin ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ke lissafawa da su a kintacen wanda zai yi nasarar zama shugaban ƙasa.

Ologbondiyan, ya ce jama’a sun gaji da mulkin jam’iyyar APC, domin sun ɗanɗana kudar su tsawon shekaru takwas, ya na mai cewa a fili ta ke cewa babu wani ɗan takarar da ya kai Atiku samun karɓuwa a duk faɗin Nijeriya, don haka a ranar zaɓe tun da sanyin safiya zai yi wa sauran ‘yan takara fintinkau.

LEAVE A REPLY