Home Home Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele

Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele

54
0
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta kawo cikas ga kokarin da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ke yi na kama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele bisa zargin daukar nauyin ta’addanci.

Alkalin kotun, ya kuma dakatar da hukumar tsaro ta SSS daga kokarin kamu ko gayyaya ko tsare gwamnan CBN a kan zargin tallafa wa ta’addanci ta bangaren kudade, tare da kyaleshi ya gudanar da ayyukan sa a matsayin gwamnan CBN muddin ba umarni su ka samu daga wata babbar kotu ba.

Kotun ta ce a kyale gwamnan CBN ya samu cikakkiyar damar gudanar da ayyukan da ke gabansa ba tare da an firgita shi ko tada ma shi hankali ba.

Kafin wannan dai, wata kotu ta yi watsi da bukatar hukumar tsaro ta DSS, inda ta ce hukumar ta koma ta samo kwararan hujjoji da shaidu kafin ta sake komawa gabanta a kan lamarin.