Home Home ‘Yan Sanda 10,000 Da Aka Yaye Za Su Yi Aiki Lokacin Zaben...

‘Yan Sanda 10,000 Da Aka Yaye Za Su Yi Aiki Lokacin Zaben Najeriya Na 2023

40
0
Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba, ya ce sabbin kananan jami’an ‘yan sanda dubu 10 da aka yaye kwanan nan, za a tura su zuwa sassan Nijeriya domin tabbatar da doka da oda lokacin zaben shekara ta 2023.

Mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta 8 Ashafa Adekunle ya bayyana haka, a wajen bikin yaye daliban makarantar horon ‘yan sanda da ke Ilori a matsayin wakilin Usman Alkali Baba.

Adekunle, ya ce bayan faretin kammala horar da sabbin ‘yan sandan, za a tura su zuwa sassan Nijeriya lokacin zabubbukan shekara ta 2023, inda za su yi aikin tabbatar da tsaro domin a gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yayin da zaben shekara ta 2023 ke kara karatowa, ana nuna damuwa a kan sha’’anin tsaro da ke kara tabarbarewa a wasu sassan Nijeriya, musamman yankin arewacin Nijeriya da ake fama da ‘yan bindiga.