Home Labaru Tirkashi: Da Wuya Nijeriya Ta Kai 2023 A Matsayin Kasa Guda –...

Tirkashi: Da Wuya Nijeriya Ta Kai 2023 A Matsayin Kasa Guda – Uma Eleazu

301
0

Wani tsohon dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar SDP a shekara ta 1993 Dakta Uma Eleazu, ya ce ba lallai ne Nijeriya ta kai shekara ta 2023 a matsayin kasa guda ba.

Eleazu, wanda ya kasance dan kwamitin da ya tsara kundin tsarin mulki na shekara ta 1999, kuma a shekara ta 2006 ya yi aiki a kwamitin da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa domin duba kundin tsarin mulki, ya ce jumhuriya ta gaskiya ce kawai za ta ceci Nijeriya.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Eleazu ya ce Nijeriya na kan turba mai cike da hatsari, don haka ya ce mai yiwuwa ‘yan Nijeriya su tsinci kansu a wani yanayi kafin shekara ta 2023.

Ya ce a yanzu mutum ba ya iya tafiya daga kudu zuwa gabas cikin kwanciyar hankali saboda yadda ake kashe-kashe babu gaira babu dalili.