Home Labaru Difilomasiyya: Za A Fara Kama Bakin Haure A Kasar Amurka

Difilomasiyya: Za A Fara Kama Bakin Haure A Kasar Amurka

197
0

Dubban mutane ne su ka shiga zanga-zanga a birnin Chicago na kasar Amurka, inda su ke sukar sabbin tsare-tsaren Shugaba Trump a kan shige da fice, yayin da ake fara samamen kama bakin-haure a ranar Lahadin nan.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar su na rike da kwalaye dauke da rubutun da ke cewa, ‘Babu yaran da za a killace,’ wato yaran da sun zama ‘yan kasa amma iyayen su bakin haure ne.

An dai gudanar da zanga-zangar ne a jajibirin ranar da aka yi niyyar kai samamen a wasu biranen kasar, domin kama wadanda ake zargin sun shiga kasar ba bisa ka’ida ba.

Matakin kama bakin hauren ya jawo iyalai da dama sun shiga fargaba da tashin hankali, kamar yadda magoya bayan bakin su ka nuna, yayin da ‘yan jam’iyyar Democrat su ka bayyana matakin da cewa tsabar mugunta ce kawai.