Home Labaru Ta’addanci: An Kashe Kawun Sanata Abbo Tare Da Yin Garkuwa Da ...

Ta’addanci: An Kashe Kawun Sanata Abbo Tare Da Yin Garkuwa Da Kishiyar Mahaifiyar Sa

267
0

Wasu mahara sun yi wa kauyen Muchilla dirar mikiya, inda su ka arce da kishiyar mahaifiyar Sanata Elisha Abbo bayan sun bindige kawun sa har lahira.

Maharan dai sun shiga kauyen da ke cikin karamar hukumar Mubi a Jihar Adamawa ne a ranar Asabar da misalin karfe 1 na rana suka yi garkuwa da matar, wadda mai jego ce kwanakin ta 11 kadai da haihuwa.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin, yayin da  wani da aka yi kisan da garkuwar a kan idon sa ya shaida cewa lokacin da ‘yan bindigar suka tasa keyar matar za su gudu da ita ne kawun sanata Abbo ya fito ya na kururuwa, lamari da ya sa ba su tsaya bata lokaci ba su ka harbe shi nan take ya fadi ya mutu.

Yanzu haka dai kauyen ya na cikin tashin hankali, na neman inda aka gudu da mai jegon da aka yi garkuwa da ita da kuma jimamin rashin kawun Sanata Abbo.

Kakakin Yada Labarai na rundunar ‘yan Sanda ta jihar  Adamawa Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin, inda tuni jami’an su sun shiga binciken yadda za a kubutar da matar tare da kamo ‘yan bindigar.