Home Labaru Tinubu Zai Magance Rikicin Arewa Maso Yammacin Nijeriya – Shettima

Tinubu Zai Magance Rikicin Arewa Maso Yammacin Nijeriya – Shettima

47
0

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya ce amfani da
karfin soji kadai ba zai magance matsalar ‘yan bindiga da
masu garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yammacin
Nijeriya ba.

Kashim Shettima ya bayyana haka ne, yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar Kano.

Yankin na Arewa maso Yammacin Nijeriya dai ya dade ya na fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wadanda kan bi mutane har gida ko su tare hanya ko su je makarantu su sace dalibai.

Kashim Shettima, ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin Bola Tinubu za ta bullo da wani shiri da ta yi wa lakabi da ‘pulaku’ domin shawo kan hare-haren da ake alakantakawa da makiyaya a yankin.

Ya ce idan dai ba so ake a cigaba da zubar da jini ba, ya kamata a sani cewa amfani da karfin soji ba zai kawo karshen rikicin Arewa maso Yamma ba.

Leave a Reply