Home Labaru Ilimi Shehun Borno Ya Bukaci Jama’Ar Jihar Borno Da Su Fito Rokon Ruwa

Shehun Borno Ya Bukaci Jama’Ar Jihar Borno Da Su Fito Rokon Ruwa

116
0

Sakamakon yadda ake fuskantar karancin ruwan sama a jihar
Borno, Mai Martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn
Umar Garbai Elkanemi, ya bukaci al’ummar musulmi a fadin
jihar su fita rokon ruwa.

Shehun Borno, ya bukaci al’ummar musulmin jihar su fito kwan su da kwarkwata domin yin addu’o’in rokon ruwa ga Allah Madaukakin Sarki.

Basaraken ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren sa Zannah Umar Ali, inda ya ce za a gudanar da sallar rokon ruwan ne a Dandalin Ramat da ke Maiduguri.

Sanarwar, ta kuma bukaci al’ummar musulmi maza da mata su halarci sallar rokon ruwan da neman taimakon Allah.

Leave a Reply