Home Labaru Kasuwanci Naira Ta Sake Faduwa Zuwa 803 Kan Kowa Ce Dalar Amurka

Naira Ta Sake Faduwa Zuwa 803 Kan Kowa Ce Dalar Amurka

74
0

Darajar takardar Naira ta sake faduwa a kasuwannin musayar
kudaden ketare a Nijeriya, bayan an canza duk Dalar Amurka
guda a kan Naira 803 a karshen mako, matakin da ke zuwa a
daidai lokacin da hauhawar farashin kayaki ke tashi.

Alkaluma sun nuna yadda farashin dalar ya kai naira 803 a kasuwannin hukuma, yayin da a kasuwannin bayan fage farashin ya kai Naira 822 a ranakun karshen mako, matakin da ke zuwa a dai dai lokacin tsadar rayuwa ke kara ta’azzara a sassan Nijeriya.

Hauhawar farashin Dala kai tsaye dai ya na shafar cinikayya a sassan Nijeriya, inda hukumar kididdiga ta kasa ke cewa farashin kayakin abinci ne kan gaba wajen hauhawa.

Duk da yunkurin Bankin CBN na samar da farashin bai-daya a kokarin daidaita kasuwar musayar kudi, har yanzu ana ci- gaba da ganin tashin farashin dala a kan mabambantan farashi a kasuwannin gwamnati da na bayan fage, inda mako bayan mako farashin ke ci-gaba tashi babu kakkautawa.

Leave a Reply