Home Labaru Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Domin Tabbatar Da Sabbin Shugabannin Hafsoshin Tsaro

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Domin Tabbatar Da Sabbin Shugabannin Hafsoshin Tsaro

76
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar
majalisar dattawa domin tabbatar da sabbin shugabannin
Hafsoshin tsaron da ya nada.

Bukatar Tinubu dai ta na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aike wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio aka kuma karanta a zauren majalisar.

A cikin wasikar, Tinubu ya ce a bisa tanadin sashe na 18 karamin sashe na 1 na dokar Sojoji ta shekara ta 2004, ya na mai gabatarwa majalisar dattawa wadanda aka nada a matsayin Hafsoshin Soji domin tantancewa.

Ya ce akwai bukatar Majalisar Dattawa ta lura da yanayin tsaron da Nijeriya ke ciki a halin yanzu, wanda ke bukatar hadin kai tsakanin ‘yan majalisa da na zartarwa domin tabbatar da tsaro mai inganci.

Leave a Reply