Home Labaru Gwamnan Jihar Borno Ya Karbi Bakuncin Tawagar Majalisar Dinkin Duniya

Gwamnan Jihar Borno Ya Karbi Bakuncin Tawagar Majalisar Dinkin Duniya

72
0

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya karbi
bakuncin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin
Duniya Amina Mohammed, da mai fafutukar goyon bayan
ilimin yara mata kuma jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya
Malala Yousafzai a Maiduguri.

A lokacin ziyarar, gwamnan ya ce gwamnatin sa ta sa dubban ‘yan matan da ba sa zuwa makaranta a wani shiri da ake ci- gaba da gudanarwa da nufin daukar ‘yan mata dubu 500 a makarantun Firaimare na Gwamnati.

Malala Yousafzai dai ta zo Nijeriya ne domin bikin cika shekaru 10 na jawabin ta na farko da ta yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma bikin ranar Malala.

A Kowace ranar 12 ga watan Yuli dai, Majalisar Dinkin Duniya ta na gudanar da bikin ranar Malala domin girmama ta, musamman a kan yadda ta yi ta fafutukar kwato ‘yancin yara da mata.

Da ya halarci bikin na karrama Malala, Gwamna Zulum ya ce ilimin yara mata shi ne babban abin da zai magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki mai dorewa, ya na mai cewa ‘yan matan da ba sa zuwa makaranta sun fi yawan yara maza da ba su zuwa makaranta a fadin jihar Borno, shi ya sa gwamnatin jihar ke matukar sha’awar shigar da ‘ya’ya mata makarantu.

Leave a Reply