Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Domin Tabbatar Da Sabbin Shugabannin Hafsoshin Tsaro

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar
majalisar dattawa domin tabbatar da sabbin shugabannin
Hafsoshin tsaron da ya nada.

Bukatar Tinubu dai ta na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aike wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio aka kuma karanta a zauren majalisar.

A cikin wasikar, Tinubu ya ce a bisa tanadin sashe na 18 karamin sashe na 1 na dokar Sojoji ta shekara ta 2004, ya na mai gabatarwa majalisar dattawa wadanda aka nada a matsayin Hafsoshin Soji domin tantancewa.

Ya ce akwai bukatar Majalisar Dattawa ta lura da yanayin tsaron da Nijeriya ke ciki a halin yanzu, wanda ke bukatar hadin kai tsakanin ‘yan majalisa da na zartarwa domin tabbatar da tsaro mai inganci.

Exit mobile version