Home Labaru Tanko Mohammed Ya Zama Shugaban Alkalan Nijeriya

Tanko Mohammed Ya Zama Shugaban Alkalan Nijeriya

204
0
Ibrahim Tanko Mohammed, Shugaban Alkalan Nijeriya
Ibrahim Tanko Mohammed, Shugaban Alkalan Nijeriya

Majalisar dattawa ta tabbatar da mai shari’a Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin tabbataccen shugaban alkalan Nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne, shugaba Buhari ya aike wa majalisar dattawa wasika, inda ya bukaci a tabbatar da Tanko Muhammad a matsayin shugaban Alkalan Nijeriya na din-din-din.

Karanta Labaru Masu Alaka: Majalisa Za Ta Tantance Ibrahim Tanko Muhammad Ranar Laraba

Shugaba Buhari ya nada mai shari’a Tanko Mohammed ne a watan Junairu, bayan dakatar da tsohon shugaban alkalan Nijeriya Walter Onnoghen bisa zargin kin bayyana kadarorin sa.

An dai haifi mai shari’a Ibrahim Tanko ne a ranar 31 ga watan Disamba na shekara ta 1953 a garin Doguwa na karamar hukumar Giade ta jihar Bauchi.