Home Labaru Majalisar Wakilai Ta Ce A Rufe Majalisar Dokokin Jihar Edo

Majalisar Wakilai Ta Ce A Rufe Majalisar Dokokin Jihar Edo

222
0

Majalisar wakilai ta ba shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS umarnin su gaggauta rufe majalisar dokoki ta jihar Edo.

Haka kuma, majalisar ta bukaci gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya fitar da sanarwa game da rikicin majalisar jihar a cikin mako guda, a kuma buga a manyan jaridun Nijeriya.

Karanta Labaru Masu Alaka: Rikici Na Kara Tsamari Tsakanin Oshiomhole Da Gwamna Obaseki

‘Yan majalisar wakilan dai sun yanke hukuncin ne bayan sun gudanar da bincike a kan rikicin majaisar jihar, wanda rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan majalisar dokoki na ya haddasa.

Wani bangare na ‘yann majalisar su na biyayya ne ga gwamna Obaseki, yayin da wani bangaren ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole.