Home Labaru Ba Da Fifikon Tsaron Arewa Maso Gabas Ya Haddasa Yaduwar Ta’addanci –...

Ba Da Fifikon Tsaron Arewa Maso Gabas Ya Haddasa Yaduwar Ta’addanci – Buhari

295
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Sakamakon maida hankalin da gwamnatin tarayya ta yi wajen tunkarar ta’addancin kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, rashin tsaro ya yadu a wasu yankunan kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka, yayin da ya karbi bakuncin kungiyar likitoci ta Nijeriya a fadar sa da ke Abuja.

Karanta Labaru Masu Alaka: An Sace Surukar Shugaban Ma’aikata Da Wata Mata A Jihar Neja

Buhari ya ce nasarorin da gwamnatin sa ta samu wajen dakusar da kaifin ta’addancin mayakan kungiyar Boko Haram, zai kara samun nasarar dakille sauran rikice-rikicen da su ka addabi sannan kasar nan.

Ya ce samar da ingataccen tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma zai cigaba da kasancewa abu mafi mahimmanci da gwamnatin sa za ta maida hankali a kai.

A karshe ya jaddada kudirin gwamnatin sa na saukaka radadin talauci ta hanyar bunkasa tattalin arziki wajen samar da ayyuka ga matasa, musamman a fannin noma, lamarin da ya ce zai yi tasiri wajen magance aukuwar miyagun laifuffuka.