Majalisar dattawa ta tabbatar da mai shari’a Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin tabbataccen shugaban alkalan Nijeriya.
Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne, shugaba Buhari ya aike wa majalisar dattawa wasika, inda ya bukaci a tabbatar da Tanko Muhammad a matsayin shugaban Alkalan Nijeriya na din-din-din.
Karanta Labaru Masu Alaka: Majalisa Za Ta Tantance Ibrahim Tanko Muhammad Ranar Laraba
Shugaba Buhari ya nada mai shari’a Tanko Mohammed ne a watan Junairu, bayan dakatar da tsohon shugaban alkalan Nijeriya Walter Onnoghen bisa zargin kin bayyana kadarorin sa.
An dai haifi mai shari’a Ibrahim Tanko ne a ranar 31 ga watan Disamba na shekara ta 1953 a garin Doguwa na karamar hukumar Giade ta jihar Bauchi.

