Home Home Takardun Bogi: Gwamnatin Kaduna Za Ta Kori Malaman Makaranta 233

Takardun Bogi: Gwamnatin Kaduna Za Ta Kori Malaman Makaranta 233

433
0

Hukumar Ilimin bai-ɗaya ta jihar Kaduna za ta kori malamai 233 da ake zargi sun gabatar da takardun makaranta na bogi.


A cikin jawabin shugaban hukumar Tijjani Abdullahi da
gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya wallafa a Facebook
ya ce an tantance takardun malamai 451 ta hanyar tuntuɓar
makarantun da malaman suka yi iƙirarin sun yi.


Shugaban ya ce bahasin da makarantu 13 suka bayar ya nuna
malamai 233 sun yi Amfani da takardun jabu.


Ya ce ɗaya daga cikin makarantar da aka tura wa takardun
malaman ta nesanta kanta da shedar karatun 212 daga cikin 233.


Hukumar ta ce za ta ci gaba da tantance sahihanci takardun
malaman jihar a matsayin ɗaya daga cikin matakan da
gwamnatin Kaduna ke ɗauka da farfaɗo da fannin ilimi.

Hukumar ta kuma ce za ta yi wa malaman Jihar 12,254
jarabawar gwaji da horo wanda za a fara daga watan Janairun
2022.

Leave a Reply