Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya yi alkawarin taimaka wa Najeriya wajen yakar ta’addanci da kuma masu tsattsauran ra’ayin addini.
Ya bayyana haka ne yayin da ya ke karbar bakuncin Jakadan
Najeriya a kasar, Farfesa Abdullahi Y. Shehu yayinda yake mika
masa takardar fara aiki a fadar Krelim.
Ya ce, kasarsa za ta yi maraba da duk wata kasa dake da alaka
da ita wajen tallafa mata ta fuskantar matsalar tsaro, domin
karfafa alakar da ke tsakaninsu.
Kazalika, Putin ya yi karin haske kan yadda COVID-19 ta kawo
tsaiko a duniya, tare da cewar kasar shi ta kammala samar da
rigakafin allurar cutar wadda za a yi amfani da shi wajen dakile
cutar.
Shugaban, ya bayyana aniyarsa na kulla yarjejeniya da kowace
kasa da ke shirin amsar rigakafin COVID-19 da kasar ta shi ta
samar.
A nasa jawabin, Jakadan na Najeriya ya nuna jin dadinsa kan
irin alakar da ke tsakanin kasashen biyu, inda ya mika sakon
gaisuwar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga Shugaban na
Rasha.














































