Hukumar Ilimin bai-ɗaya ta jihar Kaduna za ta kori malamai 233 da ake zargi sun gabatar da takardun makaranta na bogi.
A cikin jawabin shugaban hukumar Tijjani Abdullahi da gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya wallafa a Facebook ya ce an tantance takardun malamai 451 ta hanyar tuntuɓar makarantun da malaman suka yi iƙirarin sun yi.
Shugaban ya ce bahasin da makarantu 13 suka bayar ya nuna malamai 233 sun yi Amfani da takardun jabu.
Ya ce ɗaya daga cikin makarantar da aka tura wa takardun malaman ta nesanta kanta da shedar karatun 212 daga cikin 233.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da tantance sahihanci takardun malaman jihar a matsayin ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin Kaduna ke ɗauka da farfaɗo da fannin ilimi.
Hukumar ta kuma ce za ta yi wa malaman Jihar 12,254 jarabawar gwaji da horo wanda za a fara daga watan Janairun 2022.
You must log in to post a comment.