Home Labaru Takaddama: Zakzaky Zai Dawo Najeriya

Takaddama: Zakzaky Zai Dawo Najeriya

508
0

Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria Ibrahim Zakzaky ya ce zai dawo gida saboda rashin jituwar da ya samu da mahukuntan Indiya.

Rahotanni sun ce tun bayan isar sa kasar Indiya aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi, da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi.

Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta kalaman nasa, ta na mai cewa ya yi kokarin bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa, sannan ta ba gwamnatin Indiya hakuri kan mummunar halayyar da ya nuna.

A farkon watan nan ne wata kotu a Kaduna ta ba malamin da mai dakinsa Zeenat, izinin tafiya Indiya domin duba lafiyarsu bayan shafe shekara kusan hudu a hannun jami’an tsaro.

Mabiyansa da kuma masu kare hakkin dan’adam sun yi marhabin da hukuncin kotu, wanda ake ganin zai taimaka wurin kawo karshen kika-kakar da ake yi tsakanin kungiyarsa ta IMN.

Bayanin dawowar a Najeriya na kunshe ne a wani sakon bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter.

Malamin ya bayyana cewa mahukuntan yankin da ya je neman magani a Indiya sun gaya masa cewa sun yanke hukuncin mayar da shi Najeriya.