Home Labaru Ramuwar Gayya: An Kama; Dan Sandan Da Ya Ce ‘Zai Kai Wa...

Ramuwar Gayya: An Kama; Dan Sandan Da Ya Ce ‘Zai Kai Wa Sojoji Hari’

351
0

An kama wani dan sandan Najeriya bayan da ya wallafa wasu bayanai a shafin Facebook da ke barazanar cewa zai dauki fansa kan kisan da sojoji suka yi wa wasu abokanan aikin sa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar  yobe Sunmonu Abdulmaliki

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar  yobe Sunmonu Abdulmaliki, ya shaidawa kafar yada labarai ta BBC cewa ana tsare da Sunday Japhet a jihar Bauchi kuma za a ladabtar da shi, tare da sanin manufarsa akan haka.

A makon da ya gabata ne, sojoji suka kashe wasu ‘yan sanda uku da kuma farar hula guda a jihar Taraba, bayan da suka bude wuta kan wata motar bas wacce ‘yan sandan suka dauko wani mai laifi a ciki.

Mista Japhet ya fada a Facebook cewa ba zai yi wu a kashe wadannan ‘yan sandan ba haka kawai ba, kuma a bar iyalansu a cikin kunci.

Wasu rahotanni sun ce rundunar sojin kasar ta fitar da wata sanarwa da ke jan hankalin “sojojin da su yi taka-tsantsan a duk huldar da za su yi da ‘yan sanda saboda rikicin da ya faru.

Shugaba Buhari ya kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin, bayan da ya gana da shugabannin rundunonin tsaron kasar.