Home Labaru Martani: El-Zakzaky Ya Saba Dokokin Belinsa A India

Martani: El-Zakzaky Ya Saba Dokokin Belinsa A India

517
0

Gwamnatin tarayya ta ce shugban kungiyar Islamic Movement in Nigeria Ibrahim El-Zakzaky ya saba dokokin belin da kotu ta bashi kafin ya tafi kasar India neman magani.

A cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar yada labarai, Deaconess Grace Isu Gekpe ta fitar,  ya ce El-Zakzaky ya nemi a mika masa fasfo dinsa, na tafiya kasashen waje kuma ya bukaci a bar shi ya zauna Otel mai daraja ta 1 a maimakon asibitin.

Ta ce shugaban ya bukaci a bari ya tafi duk inda ya ke so, sannan a bari ya rika ganawa da kowanne irin bako da ya zo ganinsa, irin wadannan abubuwan ne suka fusata gwamnatin kasar India su ka yi barazanar mayar da shi Najeriya.

Wani sashi na sanarwar ya nemi a mika masa fasfo dinsa, amma jami’an kasar ba su amince da hakan ba, lamarin ya yi muni inda suka ki fara duba shi.

Sannan kuma El-Zakzaky ya nemi  kasar India ta janye ‘yan sandan da aka turo domin kulawa da shi, wadannan sabbin bukatun sun haifar da jinkiri wurin fara duba lafiyarsa,  inda kasar  India ta ce ba za bari ya yi amfani da kasar ta wurin tallata kungiyar sa ba.