Home Labaru TAKADDAMA: Malami Ya Bukaci Buhari Ya Tsige Magu

TAKADDAMA: Malami Ya Bukaci Buhari Ya Tsige Magu

670
0
Abubakar Malami, Tsohon Ministan Shari'a Na Najeriya,
Abubakar Malami, Ministan Shari'a Na Najeriya,

Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya aike wa shugaba Muhammadu Buhari wasikar neman ya tsige shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu, bisa wasu zarge-zargen rashawa akalla 20.

Wata majiya ta ce daga cikin zarge-zargen da Ministan ya yi wa Ibrahim Magu, akwai zargin karkatar da kudaden sata, sannan ba ya da biyayya ga na gaba da shi a gwamnati.

Majiyoyi fda dama sun ruwaito cewa, Malami ya bada jerin sunayen mutane uku da za a maye Ibrahim Magu da su, amma magoya bayan Magu da ke fadar shugaban kasa na cewa, cire Magu a wannan lokacin na iya zama babban kuskure.

Majiyoyin sun ce, abin takaici ne a ce Magu ya na fuskantar wasu miyagu da su ka rantse sai sun cire shi duk da nasarorin da ya samu, sai dai sun ce duba ga irin tuhume-tuhumen da ake yi wa ma shi, akwai yiwuwar shugaba Buhari ya bukaci kafa kwamitin bincike kafin ya yanke shawara.