Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Saki Fursunoni 6,590 A Gidajen Gyaran Hali

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Fursunoni 6,590 A Gidajen Gyaran Hali

662
0
Gwmnatin Tarayya Ta Saki Fursunoni 6,590 A Gidajen Gyaran
Gwmnatin Tarayya Ta Saki Fursunoni 6,590 A Gidajen Gyaran

Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni dubu 6 da 590 da ake tsare da su a gidajen gyaran hali daban daban da ke fadin Nijeriya.

Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya saw a hannu ya kuma wallafa ta a shafin sa na Twitter.

Malami ya ce fursunonin sun cika ka’idojin da aka gindaya na sakin su daga gidajen gyaran hali 32 da ke kasar nan, sannan ya bayyana nasarorin da ma aikatar sa ta samu daga shekara ta 2015 zuwa 2020.

Ministan ya kara da cewa, ma’aikatar sa ta taka rawar gani wajen  rage cinkoso a gidajen gyaran hali a jihohi 14 na nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a samar da hanyoyin gaggauta gudanar da shari’u domin rage cinkosu a gidajen gyaran hali sakamakon bullar annobar Coronavirus.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin  yada labarai, Femi Adesina ya bayyana haka a ranar 22 ga watan Afrilun 2020.

Haka kuma, shugaba Buhari ya aika wa shugaban Alkalan Nijeriya Tanko Muhammad waskar  roko da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa kasashe su rage cinkoso a gidajen gyran hali domin samar da tazara.