Home Labaru Takaddama: Majalisar Dattawa Ta Kalubalanci Buhari A Kan Hakkokin Taraba Da...

Takaddama: Majalisar Dattawa Ta Kalubalanci Buhari A Kan Hakkokin Taraba Da Delta

196
0

Majalisar Dattawwa ta kalubalanci fadar Shugaban kasa, bisa zargin cewa kudin da aka ba Jihohin Delta da Taraba ba su da alaka da kudin da majalisar zartarwa ta kasa ta aminta a bada.

A cikin wata wasika da ya aike wa majalisar, Shugaban kasa ya yi da’awar cewa, kudin da majalisar zartarwa ta aminta a ba Jihohin Taraba da Delta ba su su ka yarda da su ba.

Majalisar zartarwa dai ta yarda ne a kan naira biliyan 78 da miliyan 600, amma kai naira biliyan 90 da miliyan 200 a matsayin adadin kudin da su ka aminta da shi.

Mai Magana da yawun Saraki Yusuph Olaniyonu, ya ce majalisar za ta so ta yi karin haske a kan kasafin da Ma’aikatar kudi ta gabatar mata, wanda ya nuna hakin jihar Taraba ya kama naira biliyan 22 da miliyan 200, yayin da na jihar Delta ya kama naira biliyan 67 da miliyan 900.

Majilasar, ta ce ta yi bayanin ne, don kada a fada wa mutane abin da ba shi ne ba, Shugaban Kasa kuma ya farga don su na zargin makusantan sa ne ke da alhakin yi masa zagon-Kasa cikin wasikar da ya aike masu.