Home Labaru Rikicin Zamfara: Gwamnatin Tarayya Na Samun Bayanan Sirri – Garba Shehu

Rikicin Zamfara: Gwamnatin Tarayya Na Samun Bayanan Sirri – Garba Shehu

272
0

Mai magana da yawun Shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya bayyana dalilin gwamnatin tarayya na dakatar da hakar ma’adinai a jihar Zamfara.

Garba Shehu, ya ce gwamnatin tarayya ta samu bayanan sirri a kan alakar da ke tsakanin hare-haren da ake kai wa a yankin da kuma hakar ma’adinan da ake yi.

Sai dai bai bayyana irin bayanan da gwamnatin ta samu game da alakar hakar ma’adinan da kuma barnar da ke faruwa a jihar Zamfara ba, amma ya ce matakin da aka dauka ya na da alaka da matsaloliin da jihar ke fuskanta.

Ya ce ban da ‘yan Najeriya, akwai wadanda ba ‘yan kasa ba da dama da su ke aikin hakar ma’adinai, inda wasu ke yi bisa ka’ida wasu kuma ba su da lasisin yin hakan.

Garba Shehu ya kara da cewa, ya kamata mutane su yi hakuri, domin gwamnati ta na bincike kuma jama’a za su samu gamsuwa da sakamakon da za ta fitar.

Leave a Reply