Home Labaru Tattalin Arziki: Majalisar Dattawa Ta Ce Za A Shigo Da Kayan Noma...

Tattalin Arziki: Majalisar Dattawa Ta Ce Za A Shigo Da Kayan Noma Na Zamani Nijeriya

518
0

Majalisar dattawa ta ce, kudurin da za a gabatar na bunkasa harkar noma a Nijeriya zai taimaka wajen habaka tattalin arziki, zai kuma taimaka wa manoma da kayan aikin irin na zamani

A ranar Litinin da ta gabata ne, ‘yan majalisar dattawa su ka tabbatar da cewa, idan kudurin bunkasa harkar noma a Nijeriya ya tabbata, zai kawo ci-gaba sosai ga tattalin arzikin kasar nan.

A cewar Sanatocin, idan kudurin ya tabbata, zai bada hanyar fara noma na zamani a fadin Nijeriya, musamman wuraren da su ke da kasar noma mai kyau.

Da ya ke jawabi bayan ya karbi kyautar girmamawa a wani taro da ya gudana a Abuja, Sanata Sabi Abdullahi, ya ce za su kawo harkar noman zamani a Nijeriya, kuma za su rika amfani da ita a kowane lungu da sako na kasar nan, domin manoma su ci ribar abubuwan da su ke nomawa.

Leave a Reply