Home Labaru Takaddama: An Tsige Shugaban Majalisa Da Mataimakin Sa A Jihar Kebbi

Takaddama: An Tsige Shugaban Majalisa Da Mataimakin Sa A Jihar Kebbi

39
0
Majalisar Kebbi

‘Yan majalissar dokoki ta jihar Kebbi, sun tsige kakakin majalissar tare da maye gurbin shi da dan majalisa mai wakiltar mazabar Bagudo ta kudu Muhammad Abubakar Lolo.

A wata Sanarwa da majalissar ta fitar, ta ce ‘yan majalisar ashirin ne daga cikin ashirin da hudu su ka sanya hannu a takardar tsige shugaban majalissar da mataimakin sa.