Home Labaru Karin Girma: Kabiru Gayari Ya Zama Sabon Shugaban Ma’Aikatan Jihar Zamfara

Karin Girma: Kabiru Gayari Ya Zama Sabon Shugaban Ma’Aikatan Jihar Zamfara

56
0
Governor-Matawalle-appoints-Kabiru-Gayari-as-new-Head-of-Service

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya amince da nadin Kabiru Gayari a matsayin sabon shugaban ma’aikata na jihar.

Bayanin nadin, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da wayar da kan al’umma da sadarwa na jihar Yusuf Idris ya fitar.

Nadin ya biyo bayan karin girman da aka yi wa tsohon shugaban ma’aikata Kabiru Balarabe zuwa sakataren gwamnatin jihar Zamfara.

Sanarwar ta cigaba da cewa, nadin Kabiru Muhammad Gayari a matsayin Shugaban Ma’aikatan ya fara aiki nan take.