Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Takaddama: An Tsige Shugaban Majalisa Da Mataimakin Sa A Jihar Kebbi

Majalisar Kebbi

‘Yan majalissar dokoki ta jihar Kebbi, sun tsige kakakin majalissar tare da maye gurbin shi da dan majalisa mai wakiltar mazabar Bagudo ta kudu Muhammad Abubakar Lolo.

A wata Sanarwa da majalissar ta fitar, ta ce ‘yan majalisar ashirin ne daga cikin ashirin da hudu su ka sanya hannu a takardar tsige shugaban majalissar da mataimakin sa.

Exit mobile version