Home Labaru Kuma Dai: An Hallaka Kwamandan Yan Sanda Da Wasu Mutane 7 A...

Kuma Dai: An Hallaka Kwamandan Yan Sanda Da Wasu Mutane 7 A Filato

80
0
Jami'an Tsaro

Akalla mutane takwas, ciki har da babban jami’in dan sanda da dan banga aka hallaka a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Abdul-Rahman Isah dai shi ne kwamandan rundunar leken asiri ta IRT, wanda aka kashe tare da wani jami’in tsaro na ‘yan banga Hassan Mohammed.

Lamarin dai ya faru ne a a unguwar Kwoi da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Ubah Ogaba ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin wani jawabi da ya gabatar a birnin Jos.