Home Labaru Ta’aziyya: Tawagar Da Shugaba Buhari Ya Aika Ta Isa Senegal

Ta’aziyya: Tawagar Da Shugaba Buhari Ya Aika Ta Isa Senegal

136
0
Gwamnati Ba Ta Cire Dokar Hana Zirga-Zirga A Tsakanin Jihohi Ba
Sallar Idi: Gwamnati Ta Bayyana 25 Da 26 Ga Watan Mayu A Matsayin Ranakun Hutu

Tawagar Gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPC Mele Kyari ta isa Senegal domin ta’aziyyar rasuwar jagoran Dariƙar Tijjaniya a Afrika wato Sheik Khalifa Ahmed Tijjani Inyass.

A wani saƙo da mai ba shugaban ƙasa shawara kan kafofin yada labarai na zamani Bashir Ahmed, ya wallafa a shafin sa na Twitter, ya bayyana cewa cikin waɗanda suka je ƙasar yin ta’aziyyar amadadin Shugaba Buhari, akwai Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammed Babandede.

A wannan makon ne dai Marigayi Sheik Khalifa Ahmed Tijjani Inyass, ya rasu, kuma tuni aka yi jana’izar sa a birnin Kaulaha da ke ƙasar ta Senegal.