Home Labaru Kalaman Batanci: Lai Muhammad Ya Bayyana Dalilin Kara Kudin Tara Zuwa Miliyan...

Kalaman Batanci: Lai Muhammad Ya Bayyana Dalilin Kara Kudin Tara Zuwa Miliyan Biyar

226
0

Gwamnantin tarayya ta bayyana dalilan kara kudin tarar laifin kalaman batanci a Najeriya daga Naira dubu 500 zuwa Naira Miliyan 5 a dokar yada labarai da aka yi wa kwaskwarima, da nufin hakan ya zama darasi ga masu shirin aikata laifin yada kalaman batanci wadanda ka iya tada hankali.

Ministan yada labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya yi wannan bayanin a tattaunawar da aka yi da shi a nan Abuja.

A shekara 2019 ne, Shugaba Muhammadu Buhari, ya sanar da karin kudin tarar kamar yadda aka ayyana a dokokin yada labarai da aka yi wa kwaskwarima wanda kuma shugaba Buhari, ya sanya wa hannu.

Ministan ya ce sun  nemi gyara tare da kara kudin tarar ne daga Naira dubu 500 zuwa Miliyan Biyar saboda sun lura al’umma na karya dokar yadda suka ga dama musamman ganin kudin tarar ba shi da yawa, mutum na iya biyan tarar ba tare da wani matsala ba.

Ministan ya kuma kara da cewa, wasu masu neman tayar da fitina kan nemi a yada masu wasu bayanai da suka san cewa na kunshe da kalaman batanci, dan suna gadara da cewa, in ma ya zama shari’a za su iya biyan kudin tarar ba tare da wani wahala ba.

Lai Muhammad, ya ce, wadanda ke zargin gwmanati akan kara kudin ya kamata su san cewa kalaman batanci na iya rusa kasa, kuma tarihi ya nuna cewa, kalaman batancin ya rusa kasashe da dama.